速報APP / 生活品味 / Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 i

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 i

價格:免費

更新日期:2019-07-20

檔案大小:4.0M

目前版本:3.0

版本需求:Android 4.1 以上版本

官方網站:https://al-quran.app/

Email:contact@al-quran.app

聯絡地址:隱私權政策

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖1)-速報App

Al Kur’ani ko Kur’ani littafi ne wanda da Musulunci yakunshi maganan Allah (s.w.t) tsarki ya tabbata agareshi, wanda yaturo Annabi Muhammad (s.a.w) dashi zuwaga mutane gaba daya.

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖2)-速報App

Saboda amfanin masu karatun mu a duk inda suke mun ajiye littafin Allah Al-kur’ani mai girma wanda za’a dauka kuma a ajiye daga baya a karanta a lokacin bukata.

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖3)-速報App

Allah Ka bamu ladan karatun Alqur'ani.

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖4)-速報App

Allah ya sa mu cikin masu karatun Al-kur’ani mai girma da tadabburi.

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖5)-速報App

Musulunci

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖6)-速報App

Musulunci addini ne dake da mabiya a duk fadin Duniya kuma mafiya yawan su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya da yankin Afirka ta arewa wadanda mafiyansu Larabawa ne masu bin adiinin musulunci, said dai akwai dunbin mabiya addinin musulunci amo INA a fadin Duniyar mu, Ma'anar Addinin Musulunci shine " Yarda da Mika wuya ga kadaituwan Allah Madaukakin Sarki, wato Shaidawa babu abun bautawa da Gaskiya sai Allah kuma Muhammad Manzonsa ne(Ma'aikinsa ne), bayan haka ka yarda da dukkan abubuwan da ya kebanta dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai"Allah Madaukakin Sarki shi ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) da Al Kur'ani Mai Girma domin yazamo shiriya da Rahma ga Halittu baki data, an bayyana musulunci a matsayin addinin dake da saurin karin yawa a duniya a kullum wanda ke da Adadin musulmai na Duniya sun kai kusan kashi 24.1% na dukka mutanen Duniya wato fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari takwas (1,800,000,000) a fadin duniya.

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖7)-速報App

Tarihin Addinin Musulunci

Hausa Quran AUDIO - Al Kur'ani MP3 in Hausa(圖8)-速報App

Asalin addini a duniya shi ne musulunci. Mutum na farko da Allah ya halitta, Annabi Adam (alaihis salam), ya rayu ne bisa tafarkin musulunci. Dukkanin manzanni tun daga Annabi Nuhu (alaihis salam), zuwa Annabi Ibrahim, da Annabi Musa, da Annabi Isa, alaihimus salam, musulmai ne ma su kadaita Allah. Sai dai gaba dayansu Allah ya aikosu ne zuwa ga al'ummominsu kadai. Annabi na karshe kuma cikamakin tsarin annabawa shi ne Annabi Muhammadu (yabo da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da sako zuwa ga daukacin al'ummar duniya, mutane da aljannu. An haifeshi a birnin Makkah da a yanzu ke kasar Saudi Arabia. Annabi Muhammadu (SAW), bakureishe ne, dan Abdullahi da Amina daga tsatson Annabi Isma'ila (AS) dan Annabi Ibrahim (AS).